Daruruwan matasa suka fito cikin ruwan sama a Abuja dauke da kwalaye suka yi zanga zangar lumana suna bukatar shugaba Muhammad Buhari ya sauka daga mukaminsa na shugaban kasa.
A cewarsu rashin lafiyarsa taki ci taki cinyewa. Kwamred Abdul Bako Usman jigo a kungiyar Campaign for Democracy yana mai cewa tunda 'yan jarida da mataimakin shugaban kasa basu san abun dake damun shugaban kasa ba amma wasu 'yan tsiraru suna juya kasar yadda suka ga dama kamar yadda suka yi da Marigayi Musa 'Yar'Addu'a a shekarar 2010, ya zama wajibi shugaban yayi murabus.
Yace maimakon 'yan tsirarun su batawa shugaban kasa suna ya bar aikin domin a san inda kasar ta nufa.
Cikin batutuwan da masu zanga zangar suke korafi a kai shi ne cewa shugaba Buhari ya wuce kwanaki casa'in yana jinya a waje kuma a cewar Adeyanju ya sabawa kundun tsarin mulkin kasa. Yana mai cewa kudun tsarin mulki ya ba likitocinsa biyar ikon su bayyana ko zai iya cigaba da aikinsa ko kuma ba zai iya ba.
Kawo yanzu dai fadar shugaban kasa bata mayarda martani ba akan wannan zanga zangar.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5