Guinea Ta Kafa Sabuwar Gwamnati Wucin Gadi

Shugaban wucin gadi na Guinea Janar Sekouba Konate,ya kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi gabannin zabe da aka shirya gudanarwa cikin watan Yuni.

Mutane kalilan ne cikin ministoci 34 da aka bayyana sunayensu jiya litinin ne suka kasance soja,a yayinda kasar take shirin komawa tafarkin Demokuradiyya. Wan gwamnatin hada kan kasa,tana daga cikin yarjejeniyar daunin iko tsakanin masu mulkin sojan kasar da kuma 'yan hamayya.

Idan za'a iya tunawa cikin watan Disemban 2008 ne sojoji karkashin jagorancin keftin Moussa Dadis Camara suka ayyana juyin mulki. Ahalin yanzu Camara yana Burkina Faso inda yake zaman gudun hijira,bayan wani dogarinsa ya harbe ya raunata shi cikin watan Disemba. Ya yi alkwarin ba zai yi kokarin komawa kan mulki ba.