Shugaba Bush ya sake lashe zabe - 2004-11-03

Fadar white house tace dan takarar jam'iyar damokarat John Kerry, ya bada kai bori ya hau akan zaben amurka na shekara ta 2004. Mr Kerry ya amince ya sha kasa a fafatawar da sukayi da shugaba mai ci George w.Bush, wanda ke nan ya samu wa'adi na biyu na wasu shekaru hudu bayan sunyi ta tafiya kafada-da kafada a zaben.

An ce Mr Kerry ya bada sanarwar ce ga shugaba Bush sa'oi goma sha biyu bayan an rufe jefa kuri'a. Dalilin wannan kuwa shine domin, a kaucema abun da wasu ke ganin dogon jiran samu sakamakon zaben kamar yadda aka yi lokacin da Bush ya ci wa'adin sa na farko shekaru hudu da suka wuce.