Masar ta sako fursunoni fiye da dubu biyu daga gidajen kurkukun kasar, cikinsu har da daruruwan masu kishin addini.
An sako fursunonin jiya litinin daidai lokacin da aka cika shekaru 30 da yakin da kasashen Larabawa suka yi da Isra'ila a 1973.
Daga cikin wadanda aka sako har da daruruwan kungiyar Jama'atul Islamiyya wadda hukumomi suka haramta. Kungiyar ta yi ta kokarin hambarar da gwamnatin Misra a cikin shekarun 1990, kafin ta ayyana tsagaita wuta a shekarar 1997. Har yanzu akwai dubban 'ya'yanta a kurkuku.
Har ila yau an daure 'ya'yan kungiyar da dama saboda kulla makarkashiyar kashe shugaban Masar Anwar Sadat a shekarar 1981.
Masar ta saba yin ahuwa ma fursunoninta a lokacin bukukuwa domin nuna musu fatan alheri.