Sojojin Amurka Biyu, Da 'Yan Taleban Hudu Sun Mutu A Fada A Afghanistan - 2003-09-01

An kashe sojojin Amurka biyu dake Afghanistan tare da mayakan Taleban hudu a rana ta hudu ta kazamin fadan da ake gwabzawa a kusa da bakin iyaka da Pakistan.

Wata sanarwar rundunar sojojin Amurka a yankin tsakiyar duniya ta ce an kai farmaki kan sojojin Amurka jiya lahadi da tsakar rana a lardin Paktika kusa da wani sansanin Amurka.

An kashe mayakan na Taleban a gwabzawar mintoci 90 da aka yi a bayan kai farmakin.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci wani kwamandan sojojin Afghanistan a yankin yana fadin cewa a cikin kwanakin nan, mayakan Taleban su fiye da 250 sun lallaba suka shiga cikin yankin na Dai Chopan.

Tun da fari a jiya lahadin, shugaban hukumar leken asiri a lardin Zabul dake kusa da nan ya ce sojojin Afghanistan da wasyu zaratan sojojin Amurka, wadanda ke samun goyon baya da tallafin jiragen saman yaki da helkwaftoci na Amurka, sun kashe abokan gabarsu 14 cikin dare.