Babu Shaidar Cewa Koriya Ta Arewa Ta Tace Makamashin Nukiliya - 2003-07-14

Koriya ta Kudu ta ce ba ta da shaidar dewa Koriya ta Arewa ta tace makamashin nukiliya domin tsamo sinadarin Plutonium da za a iya hada makamin nukiliya da shi.

Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Yoon Young-kwan, ya ce babu wata shaidar dake nuna cewa Koriya ta Arewa ta kammala tacewa, ko ma ta fara tace rodin makamashin nukiliya da ta yi amfani da su a masana'antun nukiliyarta.

A ranar lahadi kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya ta kudu ya fara buga labarin cewa watakila arewa ta tace dukkan makamashin nukiliyar da ta sarrafa a masana'antunta.

Kamfanin ya ambaci wani mukarrabin tsohon shugaba Kim Dae-Jung yana fadin cewa ma'aikatan diflomasiyya na Koriya ta Arewa sun shaidawa jami'an Amurka a Majalisar Dinkin Duniya cewar an kammala tace makamashin ranar 30 ga watan Yuni.

Jami'an Amurka ba su ce uffan ba kan wannan rahoto.