Kasar Girka Ta Tsare Wani Jirgin Ruwa Cike Da Nakiya - 2003-06-23

Hukumomin kasar Girka sun fara bincike domin gano ko ton dari shida da tamanin na nakiyar da aka samu cikin wani jirgin ruwa jiya lahadi an yi niyyar kaiwa ne ga wata kungiyar 'yan ta'adda.

A bayan wani tsegumin da suka samu, zaratan sojoji na Girka sun tsare wannan jirgin ruwa suka shige shi a yankin ruwan kasar.

Ministan kula da zirga-zirgar jiragen ruwan kasuwanci na kasar Girka, Georges Anomeritis, ya ce takardun waibil na jirgin sun nuna cewa nakiyar ta wani kamfani ne a kasar Sudan. Amma kuma ya ce binciken farko ya nuna cewa lambar akwatin gidan waya a birnin Khartoum da aka sanya a zaman adireshin kamfanin ta karya ce.

Hukumomin Girka sun raka wannan jirgin ruwa zuwa cikin wata tasha dake Platiyali a arewa maso yamma da birnin Athens domin karin bincike.

ma'aikatan wannan jirgin ruwa, 'yan Ukraine biyar da 'yan Azerbaijan biyu, suna hannun hukumomin Girka, kuma a yau litinin za a yi musu tambayoyi.