Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, Mohammed el-Baradei, ya ce Amurka ta shawarci sufetocin makamai da su tattara kayansu su bar kasar Iraqi.
Mohammed el-Baradei ya fada a yau cewar jami'an gwamnatin Amurka sun shawarce shi da ya janye sufetocinsa daga Bagadaza, yayin da su ma sufetocin dake aiki a karkashin babban sufeton makamai na MDD, Hans Blix, aka shawarce su da su bar kasar.
Majiyoyin MDD sun ce ba za a yanke shawara kan janye sufetocin ba, har sai Kwamitin Sulhu ya nazarci lamarin nan gaba a yau litinin.
A halin da ake ciki dai, Amurka da Britaniya suna kwashe ma'aikatan jakadancinsu da ba su muhimman ayyuka daga Kuwaiti da Isra'ila, sun kuma shawarci 'yan kasarsu da su kaucewa yin tafiya zuwa yankin. A wata alamar da ake gani ta cewa yaki zai barke, 'yan kallon MDD sun bar yankin bakin iyakar Kuwaiti da Iraqi.
A wani gefen kuwa, dubban masu yin adawa da yaki sun yi gangami a nan Washington da wasu birane, suna masu bayyana rashin yardarsu da kai wa kasar Iraqi harin soja, tare da wasu dubun dubatan 'yan zanga-zanga a fadin duniya.
A nan Washington, 'yan zanga-zanga sun kunna kyandir jiya lahadi da daddare a gaban mutum-mutumin shugaba Abraham Lincoln, wanda ya shugabanci Amurka lokacin yakin basasa shekaru 150 da suka shige.
An gudanar da irin wannan gangami a kasashe da dama na duniya.
Dubban Amurkawa sun yi zanga-zanga jiya lahadi a birane masu yawa inda suke bayyana kishin kasa tare da yin Allah wadarai da jagorancin da gwamnatin Amurka take yi a yunkurin kai wa kasar Iraqi harin soja.