Taron Kolin Faransa Da Kasashen Afirka Ya Maida Hankali Kan Batutuwan Zimbabwe Da Ivory Coast - 2003-02-21

Wakilan kasashen Afirka 52 sun hallara a birnin Paris a wurin taron kolin shekara-shekara na Faransa da Kasashen Afirka da ta rena, inda batutuwan Zimbabwe da Ivory Coast suke saman ajandar wannan taro.

Kasancewar shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, wanda KTT ta dage haramcin tafiyar da ta kafa masa na wannan karon kawai, ta sa 'yan zanga-zanga sun fito kan titi yayin da wasu kasashen ke yin tur da gayyatarsa.

A jiya alhamis da aka bude taron, Kungiyar tarayyar Turai, KTT, ta bada sanarwa mai zafi tana mai kira ga shugaba Mugabe da ya mutunta hakkin bil Adama ya kuma kawo karshen cin zarafi da musugunawa abokan adawarsa.

A jawabansu wajen bude taron kolin, shugaba Jacques Chirac na Faransa da Babban Sakataren MDD, Kofi Annan, duk sun yi kira ga sassan dake yakar juna a Ivory Coast da su aiwatar da shirin zaman lafiyar da Faransa ta shiga tsakani aka kulla.