An Kawo Karshen Neman Wadanda Har Yanzu Suke Da Rai A Hadarin Jirgin Ruwan Senegal - 2002-10-01

Ma'aikatan agaji a kasar Senegal sun kawo karshen aikin neman wadanda har yanzu watakila suna da rai a hadarin jirgin ruwan fito na fasinjan kasar Senegal, wanda ya kife ranar alhamis dab da gabar kasar Gambiya, ya kuma kashe mutane kusan dubu daya.

Masu nitson da suka kai ga garwar jirgin a karkashin teku sun bayyana yadda gabobin gawarwakin dake ciki suka ringa tsinkewa a lokacin da suka yi kokarin ciro su.

Mutane 64 sun kubuta da rayukansu, dukkansu kuwa fasinja ne da ma'aikatan jirgin da suka yi waje cikin mintocin farko na abkuwar wannan hadari, suka kuma rike gefen wannan jirgi na tsawon sa'o'i har zuwa lokacin da jiragen kwale-kwale na masunta suka zo suka cece su.

An kera wannan jirgin ruwan fasinja ne domin ya dauki mutane 550 kawai. Jirgin ya kife cikin teku a lokacin da igiyar ruwa ke murdawa, hadari kuma ya taso, lokacin da ya baro yankin Casamance na Senegal kan hanyar zuwa birnin Dakar.

Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal yayi alkawarin gudanar da cikakken bincike, tare da biyan diyya ga iyalan wadanda suka mutu. Ya ce an kera wannan jirgin domin yayi tafiya cikin tabki ne kawai, ba a cikin teku ba.

Iyalan mamatan a cikin fushi tare da bacin rai, sun zargi masu gudanar da aikin jirgin da laifin yin sakaci. Akasarin wadanda suka mutun 'yan kasar Senegal ne. Sauran sun hada da 'yan kasashen Guinea-Bissau da Gambiya, da Faransa da kuma Spain.