Bam Ya Ragargaza Hedkwatar Gidan Rediyo Mai Zaman Kansa A Zimbabwe - 2002-08-29

Kafofin labarai sun bada rahoton cewa bam ya ragargaza hedkwatar wanbi gidan rediyo mai zaman kansa a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe.

Wani mai gadi guda daya ne kawai yake ciki a lokacin da bam din ya tashi, kuma an ce bai ji rauni ba.

Wannan gidan rediyon da ake kira "Muryar Jama'a", yana samowa da tsara labaransa a cikin kasar ta Zimbabwe, to amma kuma yana watso su ta mitoci masu cin dogon zango daga kasar Netherlands, domin kaucewa dokokin watsa labarai masu tsauri na kasar Zimbabwe.

Ba a san ko wanene ya dasa wannan bam ba, wanda ya yaye rufin ginin, ya kuma yi kaca-kaca da cikinsa. Ana daukar wannan gidan rediyo a zaman mai adawa da gwamnati.