Saddam Hussein Ya Ce Duk Wani Harin Da Za'a Kai Kan Iraqi Ba Zai Yi Nasara Ba - 2002-08-08

Shugaba Saddam Hussein na Iraqi yayi gargadin cewa duk wani harin da za a kai kan kasarsa ba zai yi nasara ba, ya kuma yi kiran da a kawo karshen takunkumin da MDD ta kafawa Iraqi.

A cikin wani jawabinsa da aka watsa ta telebijin domin bukin kawo karshen yakin Iraqi da Iran, shugaban na Iraqi yayi kira ga dukkan kasashen Larabawa da su fatattaki duk wani dan neman cin zali. Har ila yau yayi kiran da a tattauna a fagen diflomasiyya domin warware sabanin dake tsakanin kasarsa da Amurka.

Shugaban na Iraqi bai fito fili yayi magana kan batun ayyukan binciken makamai na MDD ba, amma kuma yayi kira ga Kwamitin Sulhun majalisar da ya maida martani ga fatawar Iraqi kan batun takunkumin tattalin arzikin da aka kafa mata a 1990.

Amurka ta ce Iraqi tana kokarin mallakar makaman kare-dangi, ciki har da makaman nukiliya.

Shugaba Bush ya ce Iraqi barazana ce ta zahiri, kuma zai nazarci dukkan hanyoyin magance wannan, ciki har da fagen diflomasiyya, matsin lamba da kuma matakan soja.