Darektan hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka, FBI, Robert Mueller, ya godewa wasu Amurkawa Musulmi a saboda abinda ya kira "taimako maras iyaka" da suka bayar wajen binciken ayyukan ta'addanci.
Mr. Mueller yayi magana jiya Jumma'a a wajen taron Majalisar Musulmin Amurka a nan Washington, duk da kiraye-kirayen da wasu suka yi masa cewar kada yayi jawabi ga taron.
Ya ce Musulmin Amurka sun bai wa hukumar FBI gagarumin goyon baya, musamman ma a lokacin da hukumar tayi rokon gaggawa na neman masu fassara a harsunan Larabci da Farisanci.
Mr. Mueller ya ce ana cacar-baki kan halartar taron majalisar da yayi jiya Jumma'a, a saboda a can baya wasu membobin Majalisar Musulmin ta Amurka sun yi jawaban bayyana goyon bayan ayyukan ta'addanci.
Amma ya ce yana da matukar muhimmanci ga hukumar FBI da Musulmi su kulla dangantaka mai karfin gaske.