Nijeriya Tayi Sabbin Jam'iyyun Siyasa Guda Uku - 2002-06-23

Hukumar zabe ta Nijeriya ta amince da sabbin jam'iyyun siyasa guda uku wadanda zasu yi takara a zabubbuka na kasa da za a gudanar cikin shekara mai zuwa.

Shugaban hukumar, Abel Goubadia, ya ce sauran jam'iyyu guda 21 da suka nemi rajista sun kasa cika ka'idojin da aka shimfida musu.

Sabbin jam'iyyun guda uku da aka yi wa rajista, sune "All Progressive Grand Alliance" ko AGPA a takaice; da "National Democratic Party" ko NDP a takaice; da kuma "United Nigeria Peoples Party" ko UNPP a takaice.

Rahotannin kafofin labarai sun ce tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim babangida mai ritaya, shine ya kafa biyu daga cikin wadannan sabbin jam'iyyu, kuma ana sa ran cewa zai kalubalanci shugaba Olusegun Obasanjo ta hanyar tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa.

Sabbin jam'iyyun uku zasu yi takara da jam'iyyu guda uku da ake da su tuni a kasar, cikinsu har da jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.