Shugaba Bush Ya Tattauna Gabas Ta Tsakiya Da Ministan Harkokin Wajen Sa'udiyya - 2002-06-14

Shugaba Bush ya ce ya rungumi abinda ya kira ganin "kafuwar kasar Falasdinu."

Shugaba Bush ya fada jiya alhamis a nan Washington cewa wannan kasa ta Falasdinu, zata bukaci cibiyoyi masu karfi ta yadda zata iya yin zaman lafiya da makwabciyarta Isra'ila.

Shugaban na Amurka ya bayyana wannan a bayan da ya gana da ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Yarima Sa'ud al-Faisal, jiya alhamis a fadar White House. Yarima Sa'ud ya ce ya ji dadin wannan kalami da ya fito daga bakin shugaban na Amurka.

Ana sa ran Mr. Bush zai gabatar da sabon shirin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya a cikin mako mai zuwa, amma kuma yayi kashedin da a guji baza rade-radi kan abinda shirin zai kunsa.