Shugabannin Afirka Sun Yi Alkawarin Warware Rikice-Rikice... - 2002-06-06

Shugabannin kasashen Afirka, sun yi alkawarin warware fitinun dake addabar yankunan nahiyar, da wanzar da mulki na gari tare da yakar bullar annobar cututtuka ta yadda, a cewarsu, nahiyar zata iya tsayuwa kan kafafunta.

Shugabannin kasashen Afirka bakwai sun yi wannan alkawari jiya laraba a wajen bude taron kolin kwanaki uku na Dandalin Tattauna Tattalin Arzikin Duniya a birnin Durban, a Afirka ta Kudu.

Suka ce kawo karshen yakin basasar shekaru hudu a kasar Kwango-Kinshasa tare ad wanzar ad zaaman lafiya a can, yana da muhimmanci wajen kara kwarin guiwar masu zuba jari kan alfanun wannan yanki.

Babban abinda taron kolin zai mayar da hankali a kai shine Sabon Shirin tattalin Arziki na Raya Kasashen Afirka, ko NEPAD, wanda shugabannin Afirka suka amince da shi a watan Oktobar bara.

Manufar shirin ita ce samo jarurruka daga kasashen waje tare da taimakon tattalin arziki, yayin da su kuma zasu tabbatar da yin mulki na gari tare da wanzar da tafarkin dimokuradiyya.