Jami'an zabe a kasar Zimbabwe, sun ce shugaba Robert Mugabe ya sake lashe zabe a wa'adi na biyar, a bayan ja-in-jar da aka yi a wannan zaben da kasashen duniya suka yi tur da shi.
Babban mai kalubalantar shugaba Mugabe, Morgan Tsvangirai na jam'iyyar MDC,yayi watsi da sakamakon zaben yana mai zargin jam'iyyar shugaban da laifin cika kawatunan zabe da kuri'un da ba na gaskiya ba. Mr. Tsvangirai ya ce sakamakon zaben shine magudi mafi muni da ya taba gani a rayuwarsa, yana mai bayyana sake zaben Mr. Mugabe a zaman "haramun."
Mr. Tsvangirai bai bayyana matakin da zai dauka nan gaba ba, illa kawai furucin da yayi cewa ba zai yi watsi da al'ummar Zimbabwe ba. Yayi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu.
Jami'ai suka ce Mr. Mugabe ya samu kashi 55 cikin 100 na yawan kuri'un da aka jefa, yayin da Mr. Tsvangirai ya samu kashi 41 daga cikin 100.
Kafofin yada labaran Zimbabwe suka ce sojoji suna zaune cikin shirin ko-ta-kwana, yayin da a yau laraba sojoji masu yawa dauke da manyan makamai suka kewaye ofishin jam'iyyar Mr. Tsvangirai a birnin Bulawayo.
Tawagar 'yan kallon zabe na Afirka ta Kudu ta bayyana wannan zabe da cewa "halaltacce" ne, amma 'yan kallon kasashen yammaci sun yi tur da zaben wanda aka fara a ranar asabar, aka kammala a ranar litinin. 'Yan kallon kasashen yammaci suka ce ba a gudanar da wannan zabe tsakani da Allah ba, kuma dubban masu jefa kuri'a a birnin Harare ba su samu damar kada kuri'unsu ba, duk da karin kwana guda da aka samu.
Har ila yau shaidu sun koka kan yadda aka musgunawa 'yan adawa da jinkiri na lokaci mai tsawo a wuraren da 'yan adawa suke da karfi.