Wata babbar kungiyar 'yan tawayen Kwango-Kinshasa ta kauracewa wani zagayen shawarwarin neman zaman lafiyar da ake yi a Afirka ta Kudu.
Wakilai daga kungiyar "Congolese Liberation Movement," wadda aka fi sani da suna MLC, sun kasa bayyana yau talata a zauren shawarwarin da ake yi a garin yawon shakatawa na Sun City. Ba a san ko masu shiga tsakani zasu gudanar da wannan zagaye na shawarwari a bayan idanun wakilan kungiyar ta MLC ba.
An bude yin shawarwari a ranar 25 ga watan Fabrairu, amma tun lokacin aka dakatar da komai a saboda rikici kan wakilcin kungiyoyin adawa na Kwango Kinshasa a zauren taron.
Kungiyar MLC tana zargin kungiyoyin adawa na Kwango Kinshasa masu dama da laifin goyon bayan gwamnati, tare da neman fifita ita gwamnati a wajen shawarwarin.
Yakin Kwango, wanda ya kunshi kasashe shida da kungiyoyin 'yan tawaye da dama, ya faro a shekarar 1998, kuma ana kiyasin cewa watakila mutane har miliyan uku suka mutu. Amma kuma a cikin shekara guda da ta shige, fada ya lafa sosai a bayan himmar sulhun da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, da kuma sauye-sauyen siyasa a cikin kasar ta Kwango Kinshasa.