Fada Ya Kaure a Kudancin Somaliya - 2002-02-18

Wani sabon mummunan fada da ya barke a tsakanin wasu bangarori biyu a garin Bardera na kudancin kasar Somalia ya sanya Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta janye ma’aikatan kasa-da-kasa daga wannan yanki.

Shedun gani-da-ido sun ce an kashe akalla mutane 15, yayin da aka jikkata wasu masu yawa a wannan fada da ya goce tsakanin sassan biyu. Wannan shine karo na biyu da aka gwabza irin wannan fada a tsakanin sassan biyu a cikin wannan Wata.

Wata mai magana da yawun MDD a birnin Nairobin Kenya ta ce majalisar tana can tana kwashe ma’aikatan wasu hukumomi daga yankin a zama wani matakin tsaro na rigakafi. An girke irin wadannan ma’aikata ne a garin Baidoa, dake da tazarar kimanin kilomita 175 arewa-maso-gabas da birnin na Bardera.

MDD ta ce, tana fatan ma’aikatan zasu koma ba da dadewa ba, saboda bala’in cuce-cuce da karancin abincin dake yin barazana ga dubban daruruwan mutane a yankin na kudancin kasar ta Somalia.