Jiragen Saman Yakin Isra'ila Sun Kai Hari A Yammacin Kogin Jordan - 2002-02-07

Jiragen saman yakin Isra‘ila sun harba makamai masu linzami kan ofisoshin hukumar mulkin kai ta Falasinawa dake Yammacin kogin Jordan. Hare-haren jiragen saman da Isra‘ila ta kai Nablus sune na biyu cikin sa‘o‘i ashirin da hudu bayan da wani dan bindigar Falasdinu ya kaiwa wasu Yahudawa uku hari inda ya kashe su har lahira.

Ana kyautata cewar firayim ministan Isra‘ila zai bukaci da shugaba Bush na Amurka ya yanke duk wata huldar dangantaka da Malam Yasser Arafat. Sai dai anji fadar shugaban Amurka ta White House na cewa shugaba Bush zai sake jaddada irin muhimmancin dake akwai na ci gaba da dangantaka tsakanin Amurka da Yasser Arafat.

A lokaci guda kuma shugaban na Amirka yace wajibi ne ga Yasser Arafat ya karfafa daukar matakan tabbatar da ganin an kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake yi.