Harin Kunar Bakin Wake a Tel Aviv - 2002-01-25

Jami’an gwamnatin Isra'ila sun bada labarin cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari tsakiyar birnin Tel Aviv, inda akalla mutum goma sha hudu sukaji rauni, biyu daga cikinsu rauni mai muni.

Jami’an tsaro na fadin dan kunar bakin wake ya dabaibaye kansa ne da wasu nakiyoyi sannan ya dunfari inda ake cin wata kasuwa a wasu kantunan wannan birnin. Ba dai kungiyar da tayi ikirarin kai wannan harin

Amma wannan harin ya biyo bayan harin da sojojin Isra’ila su kai zirin Gaza, suka kashe Bakr Hamdan wani jigo dan kungiyar Hamas, a tun daren jiya. Isra’ila ta ce shine yake da alhakin kashe wasu yahudawa kusan ishirin, yayin da Hamas tayi alkawarin sai ta dau fansar wannan kisan.