Masu saurare barkan mu da sake saduwa ta cikin wani shirin na musamman wanda shi kuma zai duba yadda ta’addanci ya shiga cikin batutuwan da kasashen duniya su ke baiwa mahimmaci tun bayan hare-haren da aka kawowa Amurka. Tun bayan hare-haren, duk wasu tarukan kasashen turai, ko na Afirka ko na nahiyoyin Amurka da Asiya suna daukan ayyukan ta’addanci da muhimmanci da kuma bullo da sabbin hanyoyi da matakan yin yaki da ta’addancin. An ga yadda kasashen duniya su ka tashi haikan su ka dauki matakai ta ko’ina, su ka rika toshewa kungiyoyin ’yan ta’adda hanyoyin samun kudaden gudanar da ayyukansu, haka kuma an ga yadda a ka yi ta daukan matakan nuna halin ba sani ba sabo akan kungiyoyin kishin addinin Musulumci irin su Hamas da "Islamic Jihad" a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma Pakistan bayan hare-haren da aka kai kan majalisar dokokin Indiya. Haka nan kuma a kasashen yankin gabashin nahiyar Asiya irin su Indonesia da Singapore da Malaysia da Philippines an dauki matakan damkwafe kungiyoyin da ake dauka na ’yan ta’adda ne. Nan da nan ita ma gwamnatin Amurka bayan hare-haren na ranar 11 ga watan Satumba, ta kirkiro da wata sabuwar hukumar da ta damkawa alhakin kulawa da harkokin tsaron cikin gida a karkashin jagorancin Tom Ridge tsohon gwamnan jihar Pennsylvania. Ga karin bayanin da atone janar na Amurka John Ashcroft ya yi a ranar da Tom Ridge ya kama sabon aikin shi na shugaban hukumar.
///JOHN ASCROFT ACT///:“The tragic events of september 11th show how critical it is to have a coordinated and a comprehensive national strategy to protect the US against...“
IBRAHIM:Abubuwan bakin ciki da takaicin da suka faru ranar 11 ga watan Satumba sun nuna bukatar a inganta sadar da cikakkun ayyukan tsaro domin a kare Amurka daga hare-haren ta’addanci.Ina yin cikakken lale maraba ga gwamna Ridge, kuma ina sa ran yin wannan aiki mai wuya dake gabanmu tare da shi da kuma kalubalen dake gaban shi.
HALIMA:Tun bayan hare-haren, a wani matakin samun cikakken goyon bayan kasashen duniya shugaba George Bush ya yi ta tattaunawa da shugabanni daban-daban ta wayar talho, sannan kuma ya rika tada manzanni takanas zuwa wasu kasashen. Haka kuma wasu shugabannin kamar Chief Olusegun Obasanjo na Najeriya, da tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, da shugabar kasar Indonesia Megawati Sukarnoputri, da prime ministan Birtaniya Tony Blair sun yi tattaki sun zo nan Amurka domin bada goyon bayansu ga Amurka. Watanni biyu bayan hare-haren na ranar 11 ga watan satumba, shugaba Bush ya je helkwatar Majalisar Dinkin Duniya a New York in da ya sake jadadda aniyar Amurka ta hada karfi da kasashen duniya su yaki ta’addanci tare, har ma ya yi jawabi kamar haka.
///BUSH ACT///:“Mr.Secretary general, Mr.President,distinguished delegates, ladies and gentlemen. We meet in a world uniting in....“
IBRAHIM:Ya babban magatakarda, mai girma shugaban babban taro,ya ku manyan baki, maza da mata, yau muna taro a lokacin da duniya ta hada kai ta yi shirin yin doguwar gwagwarmaya, za mu kare kanmu da makomarmu game da ayyukan ta’addanci da kuma tarzoma. Da ma saboda haka aka kafa Majalisar Dinkin Duniya.
///END ACT///.
HALIMA:Tun da magana ce ta kasashen duniya ai ko dole sai mun ji abun da Koffi Annan babban magatakardan MDD ya fadi a lokacin da ake kokarin kafa kawancen kasa-da-kasa na yaki da ta’addanci a duniya.
///KOFFI ANNAN ACT///:“That fight can only be won if each member state plays its part.I think the security council has given us a very.....“
IBRAHIM:Ba za ’a yi nasara a wannan yaki ba sai fa kawai idan kowace kasa ta yi abun da ya kamata ta yi.I na ganin kwamitin tsaro ya bamu kyakkyawar madogarar da za ta taimaka mana mu ci gaba sannan kuma ya aza mana harsashe ko tubalin gina kawancen da mu ke kokarin yi.
///END ACT///.
HALIMA:Tun bayan hare-haren na ranar 11 ga watan Satumbar shekarar da ta gabata,kasashen nahiyar Afirka ma ba’a bar su a baya ba, su ma sun fara daukan ayyukan ta’addanci da muhimmanci kuma ko da yake ba su da isassun kudade da kayan aikin yin yaki da ta’addanci, sun fara kamantawa. Kuma an ga yadda Amurka ta dada daukan matakan karfafa hulda da kasashen nahiyar Afirka ko da yake kasashen Somalia da Sudan na daga cikin wadanda Amurka ba ta yarda da su ba saboda ta na daukan su a zama tudun mun tsira ga ’yan ta’adda. Saboda muhimmancin musamman da Amurka ta fara baiwa kasashen Afirka tun bayan ranar 11 ga watan Satumba ne a ranar alhamis 15 ga watan Nuwanbar shekarar da ta gabata aka yi wani zaman sauraren shaida a gaban karamin kwamitin majalisar wakilan Amurka mai kula da al’amuran Afirka. Daga cikin wadanda su ka bada shaidar akwai Sulaiman Nyang na sashen nazarin al’amuran Afirka a jami’ar Howard dake nan Washington DC wanda ya yi bayani ya kuma ambaci muhimmancin kasashen Afirka irin su Najeriya, da Afirka ta Kudu, da kuma tarihin ta’addanci a Afirka. Haka ita ma Susan Rice tsohuwar karamar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da al’amuran Afirka ta bada shaida a wannan zama da aka yi. Bayan zaman ne na tattauna da ita inda na tambaye ta ko ta kaka kasashen Afirka zasu iya taimakawa cikin yaki da ta’addanci sai ta ce.
///SUSAN RICE///:“Concrete efforts to control the use of their territories by terrorists as places to operate....“
HALIMA:Su yi kokari mai ma’ana wajen hana ’yan ta’adda yin amfani da yankunansu a zama wuraren gudanar da ayyukansu, hakan ya na nufin kulawa kwarai da kan iyakokinsu, da samun damar yin amfani da jami’an karfafa doka da kuma samun sukunin tattara bayanan leken asiri da kuma musanyar bayanan da gwamnatin kasar Amurka. Sannan kuma su yi aiki tare da jami’an mu masu karfafa doka su taimaka musu wajen ganin bayan kungiyoyin ’yan ta’adda a duk inda su ke. Kamar yadda na yi nuni a cikin shaidar da na bada, mun san cewa watakila kasashen Afirka da dama suna da aniyar yin haka amma ba su da sukunin iya yin haka. Kenan wannan nauyi na taimaka musu ya na kan Amurka. Amurka ta taimaka musu cikin gaggawa kuma da muhimmanci.
///END ACT///.
HALIMA: A daidai lokacin da kawancen kasa-da-kasa su ka wargaza kungiyar al-Qa'ida, su ka kuma hambare gwamnatin ’yan Taliban a Afghanistan, haka nan su ma sauran kasashen duniya su na ta daukan matakan gano sauran rassan kungiyar Al-Qa'ida su wargaza su, da kuma kama mutane da dama wadanda ake zargi da zama ’yan ta’adda. A nan Amurka ma mutane fiye da dubu daya su na tsare ana yi musu tambayoyi, haka kuma tuni dai gwamnatin kasar Amurka ta dauki matakan tsaurara dokokin shigi da fici, da kuma kokarin gano bakin da ke nan Amurka wadanda ko dai wa’adin zaman da aka diba musu ya kare, ko kuma sun shigo kasar ce da taimakon kungiyoyin ’yan ta’adda. Babban abun la’akari a nan dai shi ne cewa hare-haren ranar 11 ga watan Satumba sun sauya tunanin kasashen duniya da na al’ummomin su game da ayyukan ta’addanci, da manufofin hulda da kasashen waje, da kuma matakan tsaro. Yanzu haka dai kasashen duniya sun hada kai su na ta kokarin ganin bayan ayyukan ta’addanci. Kuma sannu a hankali Amurka ta na ci gaba da kokarin janyo kasashen da har yanzu su ke dari-dari da batun, domin su ma su dauki ta’addanci da muhimmanci, su kuma dauki mataki. Karshen shirin kenan, a madadin Ibrahim Alfa Ahmed, da Donnie Butler, mai hada mana sauti ni ce Halima Djimrao ke yi mu ku fatan alheri. A huta lafiya.