Hukumomi A Chile Suna Kokarin Maido Da Doka Da Oda Bayan Mummunar Girgizar Kasa

Mahukunta a Chile suna kokarin maido da doka da oda da kuma raba kayan agaji a yankunan da gagarumar girgizar kasar da aka yi ranar Lahadi tafi muni.

Adadin wadanda suka rasu ya haura zuwa dari bakwai da ishirin , yayinda masu aikin ceto ke ci gaba da yunkurin zakulo mutane da gine gine suka rufe. A birnin Concepcion kusa da inda aka yi girgizar kasar mai karfin maki 8.8, wadanda suka tsallake rijiya da baya dake fama da yunwa, sun rika fasa shagunan abinci suna kwasar ganima. Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa jiya Litinin a yunkurinsu na dakatar da kwasar ganimar, wani kanti kuma ya kama wuta.

Wadansu mazauna Concepcion, birni mafi cunkoson jama’a na biyu a Chile,sun shiga gudanar da harkokin tsaro na kashin kansu,tare da killace hanyoyi da nufin tantance masu shiga unguwanninsu. An kama mutane da dama da laifin keta dokar hana yawo ko kuma sata a Concepcion da kuma yankin Maule.

Al’ummar kasa da kasa na tattara kayan agaji domin kaiwa kasar Chile. Banda abinci da matsuguni, Majalisar Dinkin Duniya tace Chile tana bukatar gadojin asibitin tafi-da-gidanka da na’urorin sadarwa, da injunan tace jini da kuma sauran kayan aikin jinya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata kai ziyara Santiago na dan gajeren lokaci a yunkurin ganin tallafin da ake matukar bukata ya isa Chile ba da bata lokaci ba.