Amurka Da Britaniya Sun Rufe Ofisoshin Jakadancinsu A Kasar Yemen

A yau lahadi Amurka da Britaniya sun rufe ofisoshin jakadancinsu dake kasar Yemen, a bisa fargabar barazana ta ta’addanci. Ofishin jakadancin Amurka a birnin Sana’a yace wannan barazana tana fitowa ne daga kungiyar al-Qa’ida ta yankin Arabiya, wadda ke da alaka da yunkurin da ya ci tura na tayar da bam cikin wani jirgin saman fasinjar Amurka ranar kirsimeti.

Amma kuma babu wani jami'i a ofishin jakadancin da ya ce an rufe ofishin ne a dalilin wata takamammiyar barazanar da aka samu.

A ranar alhamis ofishin jakadancin ya gargadi Amurkawa dake Yemen da su yi hattara sosai a saboda abinda ya kira ci gaba da fuskantar barazanar ta’addanci a kan Amurkawa a duk fadin duniya.

Britaniya da Amurka su na shirin samar da kudin kafa wata rundunar yaki da ta’addanci a Yemen, za su kuma shiga cikin wani taron kasashen duniya da za a yi nan gaba cikin wannan wata kan lamarin tsaro a Yemen.

An bayyana wadannan shirye-shiryen ne a bayan yunkurin tayar da bam cikin jirgin saman na Amurka ranar 25 ga watan Disamba. Dan Nijeriya da ake tuhuma da kokarin kai harin ya fadawa hukumomin Amurka cewa ‘yan al-Qa’ida a kasar Yemen ne suka horas da shi.