Sakatariyar tsaron cikin gidan Amurka, Janet Napolitano, ta ce babu wata alamar dake nuna cewa harin da aka yi kokarin kaiwa kan wani jirgin saman fasinja na Amurka a ranar jumma'a wani bangare ne na wata babbar makarkashiyar ta'addanci.
Napolitano ta fadawa gidan telebijin na CNN lahadin nan cewa ana gudanar da bincike.
A wata hirar dabam da ta yi da gidan telebijin na ABC, Napolitano ta ce bai dace ta yi hasashe a yanzu cewar mutumin da ake zargi da kokarin kai harin, Umar Faruk Abdulmutallab mai shekaru 23 da haihuwa kuma dan Nijeriya, yana da alaka da kungiyar al-Qa'ida kamar yadda yayi ikirari ba.
Hukumomin Amurka, sun tuhumi Abdulmutallab da laifin kokarin tarwatsa jirgin sama a lokacin da yayi kokarin sauka a birnin Detroit a nan Amurka.
Wanda ake tuhumar yana cikin jerin mutanen da hukumomin leken asirin Amurka ke sanya idanu a kansu, amma ba ya cikin jerin mutanen da aka haramtawa shiga jirgin sama a nan Amurka, abinda zai sa a hana shi shiga wannan jirgi da ya taso daga Amsterdam a kasar Netherlands.
kakakin fadar White House, Robert Gibbs, ya fadawa gidan telebijin na ABC cewa wannan lamarin ya sa jami'ai su na sake nazarin matakan sanya mutanen da ake zaton 'yan ta'adda ne cikin jerin mutanen da za a sanyawa idanu, tare da sake nazarin matakan tsaro a filayen jiragen sama.