Wani Sabon Shirin Kwamfuta Ya Gano Hanya Mai Nagarta Ta Yaki Da Maleriya

Masu bincike na Amurka sun bullo da wani sabon shiri na Kwamfuta wanda suka ce zai iya taimakawa wajen yaki da zazzabin cizon sauro ta hanyar gano sauye-sauye mafiya sauki da za a iya yi ga muhalli domin hana yaduwar wannan cuta.

Wannan sabon shirin da Kwamfuta ke nazari da aiwatar da shi, an habaka shi ne a mashahuriyar jami'ar nan ta kimiyya da fasaha da ake kira "Massachussetts Institute of Technology" ko MIT a takaice, a bayan da aka shafe shekaru hudu ana bincike a wani yanki mai fama da sauro sosai a Jamhuriyar Nijar.

Shirin yana auna yin amfani da dabarun da aka saba dauka, kamar yin amfani da gidan sauron da aka jika da magani, ya kwatanta shi da yin sauyi ga muhalli, kamar cike ramuka da kwari ta yadda ruwa ba zai iya kwanciya ba. Sauro na kaunar ruwan dake tsayawa domin nan yake yin kwai ya hayayyafa.

Injiniya na jami'ar MIT, Elfatih Eltahir, ya ce yin sauyi ga fasalin muhalli, zai taka muhimmiyar rawa a yaki da zazzabin maleriya. Ya ce a can baya, an yi amfani da dabarun yin sauyi ga muhalli, aka kuma nasarar yakar cutar maleriya a nahiyar Amurka ta Arewa da nahiyar Amurka ta kudu da kuma nahiyar turai.

A kowace shekara, cutar maleriya tana kashe mutane kusan miliyan daya, akasarinsu yara kanana. Amma Eltahir ya ce shiri na kwamfuta da suka kirkiro shi da abokan aikinsa ya zana wasu tsare-tsaren yin sauyi ga muhalli ga al'ummomin dake kokarin shawo kan yaduwar cutar zazzabin cizon sauro.

An gabatar da sakamakon wannan bincike na masanan a wurin wani taron da aka yi kwanakin baya na Kungiyar Nazarin Yanayin Muhalli ta Amurka a birnin San Francisco.