Tsohon firayim ministan
kasar Pakistan ,Nawaz Sharif, ya yanke sabon lokacin dawo da manyan
alkalan
kasar, alamarin dake wa mulkin hadin gwiwar kasar barazana.
Bayan da suka tatauna da
kananan jamiyyun mukin hadin gwiwan,
Mr sharif ya fada a yau jummaa cewa zaa
kaddamar da yarjejeniyar maida alkalan da tsohon shugaban kasar Pervez
ya kora daga aiki, wa yan majalisan
dokoki ,don su jefa kuria ranar litini.Ya kara da cewa yana saran cewa
alkalan
zasu koma bakin aiki nan da kwanabiyu.
A wata sabuwar kuma ,yan sanda Pakistan sun ce sun kama wanda suke zargin shine dan-kunar-bakin wake na uku a harin da ya kashe akalla mutane sittin da hudu a kusa da garin Islamabad.
Yan sandan sun kara da cewa, sun kwace wani riga dake dauke da nakiyoyi a wata masallaci kusa da babban masana’antar makamai da aka kaima hari a garin Wah.