"Wasan Maza" Ya Samu Karbuwa

Sabon fim din nan na Hausa wanda aka jima ana zura idanu don ganin fitowarsa, "Wasan Maza", ya fito, kuma fardusan da ya shirya shi, Bashir Abdullaji Rijau, ya bayyana cewar ya samu karbuwa a wurin ma'abuta fina-finan Hausa.

Cikin hirar da yayi da filin "A Bari Ya Huce...", Bashir Abdullahi Rijau ya ce a cikin makonni biyu suka fara bugawa. Ya ce a yanzu haka su na kokarin buga wasu faya-fayen da zasu rarrabawa 'yan kasuwar dake tallar wannan fim.

Shi dai wannan fim na "Wasan Maza" shi ne fim din Hausa na farko da aka dauka da na'urorin daukar hoto da sauti na zamani da ake kira "High Definition" a turance. Irin wannan sabuwar fasahar daukar hoto da sauti tana bayar da damar sarrafa hoto mai dan karen kyau da kuma sautin da kusan babu irinsa.

Fardusa Bashir Abdullahi Rijau ya kuma yi ikirarin cewa wannan shine fim din Hausa na farko wanda a cikinsa aka mayar da waka ta zamo mai bin bayan labari, watau labarin ne jigo.

Tuni har an fara tunanin daukar "Wasan Maza" kashi na biyu.

Sai a matsa rubutun dake saman wannan labari domin jin cikakkiyar hirar da aka yi kan "Wasan Maza" da Bashir Abdullahi Rijau.