Nijeriya Ta Kammala Wani Gagarumin Shirin Yaki da Cutar Shan Inna Ta Polio

Nijeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka, ta kammala wani gagarumin shirin kwanaki biyar na rigakafin yaduwar cutar shan inna ko Polio.

Wannan shiri na rigakafi na kasa baki daya, wanda ya samu tallafin dukkan hukumomin kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, yayi kokarin yin rigakafi ma yara miliyan 10 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa a cikin wannan lokaci.

Ma'aikatan kiwon lafiya sun bayar da maganin rigakafin cutar shan innar a yankunan arewacin kasar tare da magungunan rigakafin cututtuka kamar kyanda, tarin shika da sandarewar wuya.

Kusan dukkan wadanda suka kamu da cutar shan inna a Nijeriya su na yankin arewacin kasar ne. A shekarar 2003, an haramta bayar da maganin rigakafin na tsawon shekara a yankin arewacin Nijeriya inda Musulmi suak fi yawa bisa zargin cewa an gurbata maganin da wani abu. A bayan nan aka samu karuwar cutar sosai.