An Bukaci Nepal Da Ta Janye Umurnin Da Ta Bayar Na Harbe Masu Karya Dokar Hana Yawo

Wani kwararre kan harkokin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya ce tilas hukumomin Nepal su soke umurnin da suka bai wa jami’an tsaro na harbin dukkan masu karya dokar hana yawo, saboda umurnin ya saba da dokoki na kasa da kasa, kuma ana aiwatar da shi ne a kan mutanen da ba su san hawa ba, balle sauka.

Philip Alston ya ce ana daukar kai farmaki a kan mutanen da ba su san fari ba, balle baki, a zaman laifi na cin zarafin bil Adama.

Yau kwanaki 19 ke nan ’yan sandan Nepal suna yin arangama da ’yan rajin dimokuradiyya masu zanga-zangar neman sarki Gyanendra da ya janye kwace mulkin kasar baki daya da yayi watanni 14 da suka wuce.

A yau litinin, jami’ai sun sake kafa dokar hana yawo a rana ta biyar a jere a Kathmandu, babban birnin kasar.

A halin da ake ciki, ’yan tawaye masu akidar Mao sun kai hari kan sansanonin jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati a yankin arewa ta tsakiya. An kashe ’yan tawaye biyar da soja daya.

A wani gefen kuma, ofishin jakadancin Amurka a Kathmandu ya bukaci iyalan jami’an diflomasiyya da su bar kasar a saboda dalilan tsaro. Wakiliyar Muryar Amurka a Kathmandu, Patricia Nunan, ta ce ofishin jakadancin ya kuma umurci Amurkawa fararen hula da su bar kasar ba tare da jinkiri ba.