Hafsan ’Yan sandan Kasar Afirka ta kudu ya harbe mutane takaws sun mutu har lahira.

Hukumomin Afirka ta Kudu sun bayyana cewar wani hafsan ’yan sandan kasar ya harbe mutane takaws sun mutu har lahira. Daga cikin wadanda ya harben harda ’yan sanda hudu da kuma wani jariri guda a wani harin kai mai uwa dawabin daya rikai yi a kusa da birnin Johannesburg.

Jami‘an gwamnatin Afirka ta kudu, sun bayyana cewar a yammcin jiya litinin ne Sufiritenda Chpiia Matene ya rika harbin kan mai uwa dawabi kamar tababbe har ya kashe mata uku da jariri guda. Sannan yaje ofishin ’yan sanda inda yake aiki a Kagiso can ma ya bude wuta inda ya harbe ’yan sanda hudu.

Da aka ga yana neman ci gaba da harbe-harben ne sai ’yan sanda suka maida martani inda suka kashe Matene bayan ya jikkata kaninsa.