Mutane 6 sun mutu a Najeriya

A kallan mutane shida ne suka rasa rayukansu a nigeria a tashe tashen hankulan da 'yansanda suka danganta da ayyukan kidayar jama'a da za'a fara a wannan rana ta Talata. 'yansanda sun fadi cewar, jiya Litinin da marece ne aka sami labarin mace macen a jahar Ondo inda al'ummar yankin Irele da Ijaw suka gwabza fada tsakaninsu game da mallakar kauyen Taribo. "yan kabilar Ijaw sunyi fatali da wani shiri da gwamnati tayi na neman hada su da al'umman Irele saboda saukin kidaya.