Hukumomi Sun Tabbatar Da Gano Cutar Murar Tsuntsaye A Jihohin Katsina Da Zamfara A Arewacin Nijeriya

A ranar litinin Nijeriya ta tabbatar da cewa gwaje-gwajen da aka gudanar kan kaji daga wasu jihohi biyu da kuma birnin Abuja, sun tabbatar da kasancewar kwayar cutar murar tsuntsaye mai kisa ta H5N1.

Wakilin Muryar Amurka a Abuja, ya ambaci ministan yada labarai na Nijeriya, Frank Nweke, yana fadawa ’yan jarida jiya litinin cewar a yanzu an tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a jihohin Katsina da Zamfara, da kuma Abuja babban birnin tarayya.

Ya ce gwaje-gwajen da aka gudanar a kan kaji daga wasu jihohin guda 7 sun nuna cewar ba su dauke da kwayar cutar ta murar tsuntsaye.

Haka kuma, Nijeriya tana shirin sayen magunguna har dubu 250 na kashe kwayoyin cuta a wani yunkurin kwantar da hankulan jama’ar dake fargabar cewa annoba tana iya barkewa idan kwayar cutar ta kama bil Adama.

A yadda kwayar cutar jinsin H5N1 take a yanzu dai, za a iya daukarta ne kawai daga jikin kaza ko tsuntsuwar dake da cutar, amma ba za a iya kamuwa da ita daga mutum zuwa mutum ba.

Wani babban jami’i a ma’aikatar kiwon lafiya ta Nijeriya, Dr. Ahmed Nasidi, ya ce gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo ta taka rawar gani ya zuwa yanzu wajen takalar bullar cutar. Dr. Nasidi ya ce, "Idan aka auna kuzarin wannan kasa tare da ganin cewa shi da kansa shugaba (Obasanjo) ya sanya hannu a wannan kokarin, su kansu kawayenmu a wannan yunkuri sun ce Nijeriya ta dauki matakan kwarai cikin sauri. Sai dai abin takaici ne saboda Afirka ba ta taba fuskantar irin wannan annoba ba. Wannan shine karon farko, a saboda haka ba mu da shiri kamar na kasashen kudancin Asiya wadanda sun fuskanci irin wannan annoba a can baya sun kuma san irin matakan da zasu fi dacewa."

A halin da ake ciki, wani masanin yaduwar cututtuka a tsakanin jama’a na Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya, ya shaidawa manema labarai a birnin Kano cewa mutane a nahiyar Afirka ba zasu cutu daga murar tsuntsaye kamar mutanen nahiyar Asiya ba. Dalili, in ji shi, shine a nahiyar Asiya akwai kaji masu dan karen yawa da ake kiwo ko suke zaune a tsakiyar mutane.

Amma kuma jami’an kiwon lafiya na MDD su na fargabar cewa kwayar cutar tana iya yin zaman diris a biranen Afirka dake makare da mutane, inda kuma garkuwar jikin mutane ta lalace a saboda cutar SIDA ko rashin abinci mai amfani ga jiki.