Ma'aikatar tsaro ta Britaniya ta kaddamar da abinda ta kira binciken soja na gaggawa kan zargin cin zarafin fursunoni 'yan Iraqi da aka nuna a hotunan bidiyo.
Wata sanarwar ma'aikatar ta yi tur da dukkan ayyukan cin zarafi ko mutunci, ko nuna keta, ta kuma ce zata binciki zargin aikata su gadan-gadan.
Jiya lahadi gidajen telebijin na Britaniya sun nuna wadannan hotunan bidiyo a bayan da jaridar "News of The World" ta fito da su.
A cikin hotunan, an ga sojojin Britaniya su na dukar matasa 'yan Iraqi masu zanga-zanga da aka kama da kulakai, su na kuma kai musu bugu da kafa. Jaridar ta ce an dauki hotunan a kudancin Iraqi a cikin shekarar 2004.
Firayim minista Tony Blair na Britaniya ya fada jiya lahadi cewar za a binciki wannan lamari sosai. ya ce akasarin sojojin Britaniya dake Iraqi su na gudanar da gagarumin aiki na taimakawa Iraqi ta zamo kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya.