Hukumomi A Nijeriya Su Na Gwajin Mutanen Da Suka Kamu Da Rashin Lafiya A Yankunan Da Kwayar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Bulla

Hukumomi a Nijeriya su na gwajin mutanen da suka kamu da rashin lafiya a yankunan da aka samu bullar jinsin kwayar cutar murar tsuntsaye mai kisa kwanakin baya.

A jiya asabar jami'an kiwon lafiya a Nijeriya suka jaddada cewar har yanzu dai babu wani mutum da aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar ta murar tsuntsaye a kasar dake Afirka ta yamma. Amma suka ce kwararru su na sanya idanu a kan wasu mutanen da suka kamu da rashin lafiya a yankunan da aka tabbatar da bullar cutar a tsakankanin tsuntsaye.

An gano jinsin H5N1 na kwayar cutar ta murar tsuntsaye a wasu gonaki a jihohin Kaduna da Kano da Filato.

Jami'an Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya dake Nijeriya sun ce jami'ai su na wayar da kan jama'a a game da cutar.

Har ila yau, ma'aikatar aikin gona ta Nijeriya tana sanya idanu wajen yanka dubban tsuntsaye a arewacin Nijeriya a wani yunkuri na dakile yaduwar wannan cuta.

A halin da ake ciki, gwamnatocin kasashen waje da kungiyoyin agaji na duniya sun yi alkawarin bayar da agajin miliyoyin daloli da kayan aiki ga Nijeriya.