Firayiministan Palasdinu da ministocinsa sun sauka daga mukamansu

Firayiministan Palasdinu Ahmed Qureia da ministocinsa sun sauka daga mukamansu bayan gagarumar nasarar da kungiyar 'yan kishin Islama ta Hamas ta samu a zaben da aka yi a yankin cin gashin kan Palasdinawan. Mr. Qureia yace dolene a mutunta zaben da jama'ar palasdinawan sukayi, a kyale Hamas ta kafa sabuwar gwamnati. Ita kuwa jam'iyar 'yan Hamas wacce tayi ikrarin tasami kashi 70 na kujeru 132 da akayi takaransu, tace zata kafa gwamantin hadin guiwa da sauran jam'iyu. Hukumar zaben Palasdinu tabada sanarwar cewa tunin Hamas ta tserewa jam'iyar Fatah a yawan kuri'u.