Taron Shugabannin Kungiyar Commonwealth Zai Mayar Da Hankali Kan Batun Cinikayya

Ana sa ran cewa shugabannin kasashen kungiyar "Commonwealth" dake taron kolin kwanaki uku a kasar Malta zasu mayar da hankali a kan batutuwan cinikayya masu muhimmanci da za su maye taron Kungiyar Cinikayya ta Duniya a wata mai zuwa.

Asabar din nan ake sa ran Shugabannin na Commonwealth zasu yi kira ga kasashe masu arziki da su rage rangwamen farashin amfanin gonar da suke yi wa manomansu da kuma sauran shingayen cinikin amfanin gona dake hana kasashe matalauta da masu tasowa sayar da kayayyakinsu a kasuwannin kasashe masu arziki.

A jawabinsa na bude taron kolin ranar jumma'a, babban sakataren kungiyar ta Commonwealth, Don McKinnon, ya ce yana fata taron zai kara kuzari ga tattaunawar cinikayya ta duniya da ake yi da nufin rage talauci a duniya, wadda ta cije a yanzu.

Kungiyar Commonwealth kungiya ce ta kasashen da akasarinsu renon kasar Ingila ne. Kasashe 53 dake cikin kungiyar sun kunshi kimanin sulusin al'ummar duniya baki daya, suna kuma rike da kashi daya cikin biyar na dukkan harkar ciniki a duniya.