'Yan Shi'a Da Kurdawan Iraqi Sun Daidaita A Tsakaninsu A Kan Sabon daftarin Tsarin Mulki

Mashawartan ’yan mazhabin Shi’a sun ce su da shugabannin Kurdawa sun cimma daidaituwa a kan sabon kundin tsarin mulki na kasar Iraqi, kuma a yau litinin za su gabatar da shi gaban majalisar dokoki domin neman amincewarta.

Shugabannin bangarorin biyu tare da na ’yan mazhabin Sunni sun yi ta kokarin cimma daidaiton ra’ayi kan daftarin tsarin mulkin kafin wa’adin da majalisar dokoki ta ba su na karfe goma sha biyun daren yau litinin agogon Bagadaza.

Shugabannin ’yan Sunni sun ce ba su amince dadaftarin da ’yan Shi’a da Kurdawa suka zana ba, amma kuma da alamun ba su da yawan kuri’un da zasu iya hana zartas da wannan kundi a cikin majalisa.

’Yan Sunni suka ce idan har majalisar dokoki ta amince da daftarin tsarin mulkin, to zasu bukaci dukkan ’yan Iraqi da su ki amincewa da shi a kuri’ar raba-gardama da aka shirya gudanarwa.

Babu wani cikakken bayani a game da daftarin tsarin mulkin. An ce wani muhimmin sashe ya ayyana Iraqi a zaman Tarayya, tsarin da ’yan Sunni suka sha yin adawa da shi.

A halin da ake ciki, rundunar sojojin Amurka ta ce an kashe mata soja guda aka ji rauni ma wasu uku a lokacin da bam ya tashi dab da motar sintirinsu yau litinin a Samarra.