Bama-Bamai Sun Kashe Sojojin Amurka Hudu A Afghanistan

Wasu bama-baman da suka tashi a kasar Afghanistan, wadanda kuma ake dora laifinsu a kan 'yan tawayen Taleban, sun kashe sojojin Amurka hudu, da 'yan sandan Afghanistan biyu, yayin da wasu jami'an ofishin jakadancin Amurka su biyu suka ji rauni.

Wani bam da aka boye a gefen hanya ya kashe sojojin na Amurka su hudu, wasu uku suka ji rauni da asubahin lahadi a lardin Zabul na kudancin kasar. Wani kwamandan sojojin Amurka ya ce wannan harin bam ba zai karya musu karfin guiwa ba.

A wani bangaren an lardin kuma, an kashe wasu 'yan sandan Afghanistan su biyu a wani tashin bam mai kama da na farko.

A halin da ake ciki, wani bam ya tashi da kwambar motocin ofishin jakadancin Amurka dake shigewa a wata unguwa dake bayan gari a yamma da birnin Kabul, har jami'ai guda biyu suka ji rauni maras tsanani.

A lardin Kandahar na kudancin kasar, 'yan bindiga a kan babura sun kashe wani babban malami mai goyon bayan gwamnati, yayin da a lardin Kunar na gabashin kasar 'yan tawaye suka yi kwanton-bauna suka far ma wasu motocin tanka biyu dake dauke da man fetur zuwa wani sansanin sojan Amurka.