Ina Jin Dadin Yadda Jama'a Suka Karbi Harkar Fim Na Hausa, Har Ma Yara Sun Watsar Da Indiyanci Sun Rungumi Hausa - in ji Jaruma Rukayya Umar

Jaruma Rukayya Umar Santa, wanda mutane suka fi sani da sunan Rukayya Dawayya, ta bayyana farin cikin yadda harkar fina-finan Hausa suka samu karbuwa a wurin Hausawa, har ma a yanzu yara sai wakokin fina-finan Hausa suke yi maimakon wakokin Indiya da aka saba ji a bakinsu.

Jaruma Rukayya, wadda aka haifa a kasar Sa'udiyya, ta fadawa filin "A Bari Ya Huce..." na Sashen Hausa cewar ta fara shiga harkar fina-finai a shekarar 2001, kuma babu wadda ta ja ta sai Jaruma Saima Mohammed Raga, wadda ta ce har yanzu ita ce ke burge ta cikin wannan harka.

Jarumar ta roki gwamnatocin arewacin Nijeriya da su saki jikinsu da masu harkar fim su kuma dafa musu baya kamar yadda masu yin fina-finai a sauran yankunan Nijeriya suke samun tallafin gwamnatoci da kuma masu kudadensu. Ta ce babu shakka idan suka yi haka, to lallai harkar fim din Hausa zata habaka ta yadda al'adar Hausa ba zata taba bacewa ba.

Jaruma Rukayya Dawayya ta ce wannan harkar fina-finai sana'a ce babba, ta kuma roki Hausawa da sauran masu kallon fina-finan da su fahimce su, su kuma ringa ba su shawarwari masu kwari da zasu kai ga ci gaban wannan harka, maimakon suka da harbin iska.

Idan ana son jin cikakkiyar hirar da Jaruma Rukayya Umar Dawayya ta yi da Ibrahim Alfa Ahmed, sai a matsa rubutun dake sama inda aka rubuta "Saurari Hirar Rukayya Dawayya."