Iran Ta Balle Kwadunan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Kulle Wata Masana'antar Nukiliya Da Su

Iran ta ce ta balle kwadunan da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya a wasu sassan masana'antar tace karfin Uranium, matakin da zai ba ta damar komawa ga aiki gadan-gadan a wannan masana'anta da ake takaddama a kai a yankin tsakiyar kasar.

An bayar da sanarwar daukar wannan mataki yau laraba a daidai lokacin da majalisar zartaswar Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya ta dage taron gaggawa a birnin Vienna kan batun matakan na Iran. Hukumar ta ce ma'aikatan diflomasiyya suna tuntubar junansu a wani yunkuri na cimma daidaiton ra'ayi kan irin martanin da za a mayar.

A watan Nuwambar bara, Iran ta yarda zata dakatar da aikin tace karfen Uranium a wannan ma'aikata dake Isfahan, domin magance zarge-zargen da Amurka da Turai suke yi cewar tana kokarin kera makaman nukiliya ne a asirce.

Kungiyar Tarayyar Turai, tare da goyon bayan Amurka, ta yi barazanar gurfanar da Iran a gaban Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya domin a nazarci kafa mata takunkumi idan har ta koma ga aikin tace karfen na Uranium.

Kwamitin Sulhu yana iya kafawa Iran takunkumi idan har ya gano cewar ta karya Yarjejeniyar Dakile Yaduwar Makaman nukiliya.