Alhamdu Lillahi, Yanzu Jama'a Sun Fara Fahimta Da Rungumar Ayyukanmu-In Ji Jarumi Ali Nuhu

Shahararren dan wasan fim na Hausa, Jarumi Ali Nuhu, ya bayyana gamsuwar yadda a yanzu jama'a suke kara nuna fahimta da kuma rungumar fina-finan Hausa da su kansu 'yan wasan, mazansu da matansu.

A cikin hirar da yayi da filin "A Bari Ya Huce..." na Sashen Hausa, Ali Nuhu ya ce a yanzu su kansu 'yan wasan fina-finan na Hausa da kamfanonin dake shiryawa ko daukar nauyin wadannan fina-finai suna watsar da irin bahaguwar akidar nan ta yin gaba da juna, suna rungumar junansu a zaman 'yan'uwa.

A lokacin da yake bayyana yadda aka yi har ya shiga cikin wannan harka ta fina-finan Hausa. Jarumi Ali Nuhu ya ce tun yana dan yaro yake sha'awar kallon fina-finai, kuma a lokacin da yake karatu a Jami'ar Jos sai ya fara shiga cikin wasannin kwaikwayo a gidajen telebijin a Jos din.

A bayan da ya kammala karatunsa, ya kuma yi aikin hidimar kasa a Ibadan, sai ya komo Kano, inda ya fara shiga harkar fim kafin ya samu wani aikin yi. Amma kuma irin karbuwar da ya samu a cikin wannan harka ta Fim din Hausa, ta sa ya watsar da batun neman wani aikin, ya koma fim baki daya.

Fim din farko da jarumin ya fara yi a shekarar 1999, shine "ABIN SIRRI NE" inda a ciki ya taka rawar mutane biyu, Jamilu da kuma Faisal.

An haifi Jarumin a shekarar 1974 a Maiduguri a Jihar Borno, amma kuma ya girma ne a Kanon Dabo.

Domin jin cikakkiyar hirar da Jarumin yayi da Ibrahim Alfa Ahmed sai a matsa rubutun dake saman wannan labari.