Wani Sabon Rahoto Yace Agajin Da Amurka Ta Ke bai Wa Afirka Bai Karu Kamar Yadda Shugaba Bush yake Ikirari Ba

Wani sabon rahoton da wata cibiyar bincike dake nan Washington ta bayar ya ce yawan agajin da Amurka ta ke bai wa kasashen Afirka a karkashin gwamnatin shugaba Bush bai karu kamar yadda shugaban yayi ikirari ba.

Rahoton na cibiyar da ake kira "Brookings Institution" ta ce idan aka yi la'akari da yawan hauhawar farashin kayayyaki, agajin da Amurka ta ke bai wa kasashen bakar fata na Afirka ya karu ne da kashi 56 daga cikin 100 a shekaru hudu da suka shige. Shugaba Bush kuwa cewa yayi yawan agajin da Amurka ke bai wa nahiyar ya karu da kashi dari biyu daga cikin 100 ne, ko kuma ya ninku sau biyu ke nan.

Amma kuma rahoton cibiyar ta Brookings ya ce agajin raya kasa na zahiri, wanda bai shafi agajin abinci da na tsaro ba, ya karu da kashi 33 ne kawai daga cikin 100 daga shekarar dubu biyu zuwa dubu biyu da hudu.

Firayim ministan Britaniya, Tony Blair, yayi kira ga kasashe masu arziki da su ninka yawan agajin da suke bai wa Afirka, shirin da bai samu goyon baya sosai ba daga hukumomi a nan birnin Washington.

Babbar marubuciyar wannan rahoto ita ce Susan Rice, tsohuwar mataimakiyar sakataren harkokin waje mai kula da al'amuran Afirka a gwamnatin shugaba Clinton.