Tsohon shugaban sojin Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida wanda aka fi sani da IBB ko yana Shirin kaddamar da littafin da ya wallafa akan rayuwar shi a ranar 20 ga watan Fabrairun 2025.
A zauren Congress Hall na hotel din Hilton Hotel ne za a yi Taron kaddamar da littafin da aka lakabawa “A journey in Service” wanda za a iya fassara shi da “Rayuwar Hidima”
Wannan na zuwa bayan tsawon shekaru 32 da IBB ya sauka daga karagar mulkin Najeriya a dalilin matsin lamban da ya sha bayan da ya soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 da ya nuna cewa marigayi Moshood Abiola Olawale da aka fi sani da MKO ne yake kan gaba a zaben.
Shekaru 8 din da Babangida ya shugabanci Najeriya suna tattare da batutuwa masu daure kai da suka sa akayi ta sukar lamirin dokokin gwamnatin shi sannan gwmanatin shi ta yi ta kama masu rajin kare hakki bil-Adama.
Sauran abubuwa masu daure kan da suka dabaibaye mulkin shi sun hada da kasa gano makisan shahararen dan jaridar nan Dele Giwa da soke zaben 12 ga watan Yunin 1993.
Karkashin shugabancin Babangida ne aka kirkiro Shirin gyara tattalin arziki da aka fi sani da SAP a takaice, wato Structural Adjustment Programme, wanda yayi sanadiyar tawaye a fadin kasar.
IBB yayi hiraraki da kafafen yada labaran cikin gida da na kasashen waje tun bayan saukar shi daga kujerar mulkin Najeriya, yayi kokarin kaucewa batutuwa masu sarkakiya da suka faru a lokacin da yake Mulki.
Kimanin shekaru 7 da suka gabata, ya bayyana shakku kan wallafa littafi yana mai cewa, bashi da tabbacin ko ‘yan Najeriya “zasu so su karanta littafin da mai mulkin kama karya ya wallafa ba”. Ko da yake daga bisani ya bada kai bori ya hau.
Ya kuma kara da cewa, al’umma sun masa gurguwar fahimta, sannan ya ambaci rawar da ya taka a zaben 12 ga watan Yunin 1993 da kuma wasu dokokin da gwamnatin sa ta samar tsakanin 1985 zuwa 1993 a matsayin shugaban kasar soji.
Ana sa ran shugaba Bola Ahmad Tinubu shi ne zai jagoranci sauran shugabannin Najeriya da takwarorin su daga makwabtan kasashen Afirka a wurin taron kaddamar da littafin da aka dade ana dakon shi.
Bayananan da aka aikewa manyan bakin da aka gayyata sun nuna cewa kwamitin Amintattun gidauniyar dakin karatun shugaban kasa y ace za a kaddamar da littafin tare da kaddamar da asusun neman tallafin gina dakin taron shugaban kasar.
Shugaba Olusegun Obasanjo ne zai shugabanci taron kaddamar da littafin yayin da tsohon shugaban Ghana Nana Akufo Ado kuma zai gabatar da jawabi na musamman. Tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo shine zai