A yau Alhamis, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ke alhinin mutuwar sojojin suka mutu sakamakon harin da aka kai kan sansaninsu da ke Sabon Gida a yankin Damboa na jihar Borno.
Tinubu a sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana tausayawarsa ga hukumomin sojin kasar sakamakon rashin zaratan dakarunsu 6 yayin wani harin da aka kai musu a ranar 4 ga watan Janairun da muke ciki.
"Ina mika godiya da alhinina ga hukumomin soji dana tsaron kasarmu a madadin al'ummarmu mai cike da godiya.
"Sadaukarwa da jajircewarku ba za su tafi a banza ba, kuma muna goyon bayanku a kokarin da ku ke yi na magance barazanar tsaro".
Babban hafsan mayakan Najeriyan ya kuma yabawa dakarun kasar saboda daukar tsauaran matakan gaggawa musamman bangaren mayakan sama, daya kai hare-haren ramuwar gayya.
Ku Duba Wannan Ma Shelkwatar Tsaro ta Tabbatar Da Mutuwar Sojoji 6 A Harin Borno