A cewar wani mazaunin yankin, mai su na Hon Iliyasu Salisu, ‘yan bindigar sun kai hari hare a kauyukan Manya, Kabaso, Yalwa, Bafada, Kuda, Makini da kuma Sabuwar Tunga inda ya ce, sun kashe masu Mutane 17.
Iliyasu ya ce, ‘yan bindigar masu tarin yawa sun isa kauyukan ne a cikin motoci da babura, motocin sun hada da kanta guda goma da Golf 10 da motar Kurkura (Isuzu) guda biyar, wadanda su ka yi amfani da su wajen kwashe kayan abinci da kuma mutanen da su ka yi garkuwa da su.
“Sun dauki mutum Dari Biyar da Ashirin da Daya (521). A Manya sun kashe mutum 7 sun dauki mutune 200, a Kaboso sun kashe mutum 5 sun dauki 200, sai Yalwa sun kashe mutum 2 sun dauki mutune 50, a kauyukan Bafada da Kuda sun dauki mutune 50 sun kashe mutum daya daya,” inji Hon Iliyasu Salisu.
Shi kuwa Shehu Danfodio, wanda shi ma an dauki dangin shi a yayin harin, ya ce an kwana an wuni ana yi, ya ce, suna neman dauki daga mahukunta don a ceci rayuwarsu.
“Tun misalin karfe uku da rabi a ranar Talata suka shigo mana, sun kashe mutane sun dauki wasu sun kwashe mana kayan abinci, kuma suka sake dawowa ranar Laraba. Duk inda kabi za ka ga mutane, wani wajen gudu ya fadi ya karye, wani kuma ka gan shi kwance ya mutu, ya kamata hukumomi su kawo mana dauki su ceci rayuwr mu, tashin hankalin yayi yawa.” Inji Malam Shehu.
Da yake bada tabbacin faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar mulkin Maru, Alh Bello Muhammad Jabaka, ya ce, ‘yan bindigar sun kashe mutane a kauyukan kuma sun dauki mutane sama da dari uku duk da ba su da cikakkun alkaluman yawan mutanen da ba a gani ba da wadanda aka kashe.
“Mu na nan mu na ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan lamarin tsaro don ganin an samu kwanciyar hankali a yankin da ma sauran sassan jihar, kuma na tura a yi cikakken bincike don sanin kididdigar barnar da su ka yi mana a yankin,” cewar shugaban karamar hukumar mulkin Maru, Alh Bello Jabaka.
Ya zuwa yanzu dai rahotanni daga yankin na nuni da cewa, akwai mutane da yawa da ba a ma gano inda suke ba, yayin da wasu sun bar yankin sun samu mafaka a wasu garuruwan.
Saurari cikakken rahoton Abdul'aziz Bello Kaura:
Your browser doesn’t support HTML5