Jakadun Tarayyar Turai Sun Amince da Sake Kakabawa Rasha Wani Sabon Takunkumi

Russia

Shugaban kasar Hungary yace Jakadun Tarayar Turai sun amince da kakabawa Rasha sabon takunkumi saboda yakin da Rasha take yi da Ukraine, kuma zai kaikaici akasarin manya-manyan jiragen ruwan Rasha.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, an sanya sabbin takunkumin ne a kan jiragen ruwan Rasha kusan 50 wadanda Rasha ke amfani da su wajen jigilar Mai.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen ta ce "Ina maraba da amincewa da sabon takunkumi, wanda ya kaikaici jiragen ruwan Rasha."

Takunkumin, wanda ake sa ran za a amince da shi a hukumance a ranar Litinin mai zuwa, ya hada da wasu kamfanoni da daidaikun mutane.

Jerin takunkumin da kungiyar Tarayyar Turai mai mambobi 27 ta kakabawa Rasha a halin yanzu ya hada da mutane da hukumomi sama da 2,000. Wanda ya hada da hana tafiye tafiye da kuma kwace kadarorin shugaban Rasha Vladimir Putin da mukarrabansa da kuma wasu 'yan majalisar dokokin kasar da dama.

Kungiyar EU ta fara sanya takunkumin ne bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine kusan shekaru uku da suka gabata.