Kungiyoyin Sa-Ido Na Kasa Da Kasa Sun Yaba Da Zaben Ghana

Kungiyoyin Kasa Da Kasa Masu Sa Ido Kan Zaben Ghana

Kungiyoyin sun yabawa Ghana da ‘yan kasar bisa gudanar da zaben Shugaban kasa da na Majalisun dokoki cikin lumana.

Kungiyoyin da suka fito daga Tarayyar Afirka (AU), Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), da kungiyar Commonwealth a wani taron manema labarai na hadin gwiwa, sun yaba wa hukumar zabe (EC), jami’an zabe, jam’iyyun siyasa, ‘yan sanda, da kafafen yada labarai kan rawar da suka taka wajen tabbatar da nasarar gudanar da zaben a Ghana.

Kungiyoyin Kasa Da Kasa Masu Sa Ido Kan Zaben Ghana

Da take jawabi a taron manema labaran a Accra babban birnin Ghana, Sahle-Work Zewde, tsohuwar Shugabar kasar Habasha kuma Shugabar tawagar sa ido kan zabe a Tarayyar Afirka (AUEOM) ta ce, an gudanar da zaben cikin lumana da kara tabbatar da dimokuradiyyar kasar. Tace, ‘Tawagar masu sa ido a zabukan kasashen tarayyar Afirka (AUEOM) ta yabawa al'ummar Ghana bisa jajircewar da suka yi na tabbatar da tsarin dimokuradiyya, wanda hakan ke nuni da yadda aka gudanar da babban zaben kasar a ranar 7 ga watan Disamban 2024 cikin lumana. Gaba daya tsarin zaben ya bi ka'idodin yankin kasa da kasa, da kara karfafa kimar dimokradiyyar Ghana.

Alhaji Mohammed Namadi Sambo, tsohon mataimakin Shugaban Najeriya kuma jagoran tawagar sa ido a kungiyar ECOWAS, yace masu kada kuri’a sun yi zabe cikin yanayi mai kyau, ba tare da tsangwama ko takurawa ba. Ta kuma taya al'ummar kaar Ghana murna. ‘Tawagar masu sa ido kan zabe ta Ecowas na taya al'ummar Ghana murna, tare da yi musu fatan ci gaba da samun zaman lafiya, daukaka, da ci gaba."

Kungiyar sa ido ta ECOWAS ta jinjinawa Shugaban Ghana mai barin gado, Nana Akufo-Addo bisa yadda ya jagoranci kasar na shekaru 8, daya daga cikin mambar kungiyar.

Kungiyar sa ido ta Commonwealth a karkashin jagorancin tsohon Shugaban kasar Botswana, Dokta Mokgweetsi Masisi tace, sun lura an bai wa nakasassu da tsoffi fifiko kuma an ba wa masu fama da matsalar gani da ido hakkinsu a wasu rumfunan zabe. Sai dai kuma sun lura da kalubale a wasu rumfunan zabe don wurin kada kuri'a ya yi wa masu amfani da keken guragu nisa.

Ya kara da cewa, ‘Rahoton su na karshe mai dauke da muhimman shawarwari za su mika shi ga babban sakatare kuma a raba shi zuwa ga gwamnatin Jamhuriyar Ghana da sauran masu ruwa da tsaki da sauran jama'a.

Kungiyoyin Kasa Da Kasa Masu Sa Ido Kan Zaben Ghana

A gefen taron, tsohon mataimakin Shugaban Najeriya, kuma jagoran tawagar kungiyar ECOWAS ya yabawa hukumomi da al’ummar Ghana bisa yadda aka gudanar da zaben kan tsari, a hira ta musamman da Muryar Amurka. Ya kara da cewa, ya yabawa mataimakin Shugaban Ghana kan amincewa da shan kaye a Zaben, kuma ya taya John Mahama murna, wanda ya lashe zaben.

Alhaji Namadi Sambo ya ce, yadda ‘yan takara ma suka gudanar da yakin zabensu ma abin koyi ne ga kasashen Afirka, domin sun yi shi ne bisa ga bukatun al’umma, ta hanyar bayyanawa jama’a yadda za su biya musu bukatunsu idan an zabe su.

Tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama, na babbar jam’iyar adawa ta NDC, wanda ya lashe zaben Ghanan da kashi 56.55 cikin 100 na kuri’un da aka kada, ya yi jawabin amincewa da nasararsa bayan da hukumar zabe ta ayyana shi, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar a hukumance.

Saurari cikakken rahoton Idriss Abdallah:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Sa-Ido Na Kasa Da Kasa Sun Yaba Da Zaben Ghana