Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya EFCC ta umurci jami’an ta su dau matakin binciken hatta gwamnonin da ke kan gado kan aiyukan almundahana.
Wannan na daga cikin matakan da hukumar ta dauka bayan nasara a kotun koli kan gwamnonin nan 19 da suka kalubalanci hurumin kafa hukumar da kuma samar mata kudin gudanarwa.
Shugaban hukumar Ola Olukoyede ya ce hukuncin kotun da ya kori bukatar gwamnonin 19 da gwamnan Kogi Usman Ododo ya ke kan gaba wajen neman Kotu ta soke hukumar ya dada basu kwarin gwiwa.
Olukoyede ya ce jami’an EFCC suna da dama su tattara bayanan tuhumar gwamnonin da ke kan kujerar mulki amma baza a dau wani mataki akan su ba har sai bayan wa’adin gwamnonin ya kare kafin a gurfanar da su a gaban kotu.
A dalilin kariyar da doka ta baiwa gwamnonin ya sa mai baiwa shugaba Tinubu shawaraka akan sadarwa Bayo Onanuga ya dora alhakin boye tsohon gwamna Yahaya Bello wanda yanzu yake fuskantar sabuwar tuhuma ta zargin badakalar Naira biliyan 110 akan gwamna Ododo mai ci yanzu.
A latsa na don a saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5