Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta harba makaman mizile guda 120 da jirage marasa matuka 90, a wani farmaki mai girma da ta kai a fadin Ukraine inda ta auna wuraren samar da makamashin ta.
Yau Lahadi, Zelensky ya ce, Rasha ta kai farmaki da samfirin jirage marasa matuka daban daban cikin su har da samfirin Shahed, makaman mizile masu sarrafa kansu da makamai masu cin dogon zango.
Ya ce na’urorin kare hare haren saman Ukraine sun kakkabo jirage marasa matuka 140.
Tun bayan da ta fara mamayar ta gadan gadan a kasar dake makwabtaka da ita a watan Fabrairun 2022, Rasha tayi ta auna cibiyoyin samar da makamshin Ukraine, lamarin da ya sa kasar ta tsinci kanta cikin yanayin gaggawa wanda ya jefa kasar baki daya cikin duhu bayan da lantarki ya katse.
Wannan farmakin aka kai da jirage marasa matuka da makaman mizile, su ne farmakin da Rasha ta kai mafi girma cikin watanni 3.